Wani Pastor ya tafi sama zuwa Aljanna domin kamawa jama'ar sa ɗaki, guzurin soyayyun kaji
Kamar yadda zaku gani ga mabiyansa ne suka ɗaga shi sama yana ƙoƙarin shiga cikin rufin Silin inda ta nan ne zai fasa rufin kwano ya wuce can sama zuwa Aljanna don ya kama musu gidaje kamar yadda yace.
Faston kafin ya tafi saida ya umarce su da su haɗa masa guzurin abincin da zai riƙa ci a kan hanyar zuwa aljannar kafin ya dawo.
Tuni mabiyan sa, suka siyo gasassun kaji da balangu da tsire mai zafi da ruwan roba da kayan marmari suka aje masa a cikin rufin Silin ɗin idan yaje sama