Ka/ki burge budurwarka/saurayinki da yaren kasuwar canjin kudi.


Humbleguy882022/01/22 09:57
Follow

Ka/ki burge budurwarka/saurayinki da yaren kasuwar canjin kudi.

WikiFX APP  |   2021-12-28 15:06:37

 Kamar yadda a kowacce sabuwar fasaha daka koya, kana bukatar ka koyi yaren musamman idan kana son kayi nasara wajen sace zuciyar wanda kake so.

 Kai, sabon dan koyo, dole kasan abubuwa kamar bayan hannunka kafin kayi cinikayyarka ta farko.

 Wasu daga cikin wadannan abubuwa kariga kasansu, amma baya taba cutarwa dan ka dan kara nazari akai.

image_stage6.png

 Manya da kananan kudade

 Kudade guda takwas da akafi yin cinikayya dasu (USD, EUR, JPY, GBP, CHF, CAD, NZD, DA kuma AUD) su ake kira da suna “manya.” Wannan su akafi yawan cinikayya dasu kuma sukafi bada sha’awa.

 Duk gaba daya ragowar kudade ana kiransu da suna kananan kudade.

 Kudade masu Tushe

 Kudi mai tushe shi ne kudi na farko a kowanne jerin kudade biyu. Farashin kudi yana nuni da yadda kudi mai tushe yake da daraja idan aka auna akan kudi na biyu.

 Misali, idan farashin USD/CHF yayi daidai da 1.6350, to dala daya tayi darajar 1.6350 CHF.

 A kasuwar canjin kudi, dalar Amurka ana daukanta a matsayin “tushen” farashishshikan kudi, ma’ana ana bayyana farashishshikan a matsayin rabo daya na dalar Amurka akan kowanne farashin kudade jeri biyu.

 Togaciya ta farko akan wannan dokar shi ne fam din Birtaniya, EURO, dakuma dalar Australia da ta New Zealand.

 Kudin da aka sakawa Farashi

 Kudin da aka sakawa farashi shi ne kudi na biyu a kowanne jerin kudade biyu.

 Yawanci ana kiransa da kudin pip sannan kuma kowacce riba ko asarar da ba’a gane mata ba ana nunata acikin kudin.

 Pip

 Pip shi ne rabo daya mafi kankanta na farashin kowanne kudi.

 Kusan kowanne jerun kudade biyu sun hada da muhimman lambobi guda biyar kuma yawancin jerin biyu biyu sunada digo a take a bayan lamba ta farko, ma’ana, EUR/USD daidai yake da 1.2538.

 A wannan lokacin, pip guda daya daidai yake da canji mafi kankanta na lambobi hudu bayan digo- wato, 0.0001.

 Saboda haka, idan kudin da aka sakawa farashi a kowanne jerin kudi biyu shi ne USD, to pip daya akoda yaushe daidai yake da kaso 1/100.

 Sanannun togiyoyi sune jerin biyu byu da suke dauke da kudin Japan yen, a inda kowanne pip daidai yake da 0.01.

 Pipette

 Kaso daya cikin goma na pip. Wasu dillalan suna saka farashin pips murabba’ai ko pipettes, saboda karin sahihanci a wajen sa farashi.

 A misali, idan EUR/USD ya motsa daga 1.32156 zuwa 1.32158, to ta motsa pipettes guda biyu.

 Sa Farashin

 Sa farashi shi ne farashin da kasuwa ta shirya zata sayi kayyadadden jerin kudade biyu a kasuwar canjin kudi.

 A wannan farashin, dan kasuwa zai iya sayar da kudi mai tushe. An nuna hakan a barin dama a batun da aka kawo.

 A misali, a batun GBP/USD 1.8812/15, farashin da aka saka shi ne 1.8812. Hakan yana nufin ka sayar da Fam din Birtaniya guda daya akan dalar Amurka 1.8812.

 Farashin tambaya/nuna nufi

 Farashin tambaya/nuna nufi shi ne farashin da kasuwa ta shirya domin ta siyar da kayyadadden jerin kudade biyu a kasuwar canjin kudi.

 A wannan farashin, zaka iya siyan kudi mai tushe. An nuna hakan a barin dama a batun da aka kawo.

 A misali, a bayanin EUR/USD 1.2812/15, farashin tambaya shi ne 1.2815. Hakan yana nufin zaka iya siyan euro daya akan dalar Amurka 1.2815.

 Farashin tambaya shi ake kira da farashin nuna nufi.

 Shimfidar sa farashi-farashin tambaya

 Shimfida shine bambancin da yake tsakanin sa farashi dakuma farashin tambaya.

 “Babban adadin da aka rawaito” shi ne yanayin fuskar dillali wanda yake nufin yan lambobi na farko na farashin canji.

 Yawanci ana rage wadannan lambobi a ruwayoyin dillali.

 Misali, farashin USD/JPY zai iya kasancewa 118.30/118.34, amma za’a rawaito a baki batare da lambobi ukun farko ba a matsayin “30/34”.

 A wannan misalin, USD/JPY sunada shimfidar 4-pip.

 Ruwayar Al’ada

 Farashin canji a kasuwar canjin kudi ana nunashi ne ta hanyar wannan tsarin:

 Kudade masu Tushe / Kudaden da aka sawa Farashi = sa farashi / farashin tambaya

 Farashin mu’amala.

 Muhimmin halin shimfidar sa farashi/farashin tambaya shi ne cewa shi ne dai farashin mu’amala na cikakkiyar cinikayya.

 Cikakkiyar cinikayya tana nufin cinikayyar saya (ko sayarwa) kuma cinikayyar siyayya ta biyan diyya (ko sayarwa) masu girma daya a jerin kudade daya.

 A misali, a harkar farashin EUR/USD na 1.2812/15, farashin mu’amala 3-pips ne.

 Dabarar lissafa farashin mu’amala ita ce:

 Farashin mu’amala (shimfida) = Farashin tambaya – Sa farashi

 Kudaden Ketare

 Kudin-ketare shi ne kowanne irin jerin kuddade biyu wanda babu dalar Amurka a cikinsu.

 Wannan jerin kudade biyu suna nuna halayen farashi barkatai a sakamakon dan kasuwar ya fara cinikayya guda biyu ta USD.

 A misali, fara dogon (siyayyar) EUR/GBP daidai yake da siyan jerin kudade biyu na EUR/USD dakuma sayarda GBP/USD,

 Jerin kudade biyu na ketare yawanci yana daukan farashin mu’amala mai tsada.

 Jingina

 A yayin daka bude sabon asusun jingina a tareda dillalin kasuwar canjin kudi, dole ka ajiye mafi karancin adadi a wajen dillalin.

 Wannan mafi karancin adadin ya bambanta ne daga dillali zuwa dillali kuma zai iya farawa daga dan karamin adadi na $100 izuwa babban adadi na $100,000.

 A duk lokacin daka aiwatar da sabuwar cinikayya, wani Kason na ma’aunin asusu wanda yake cikin asusun jingina za’a ajiye shi a gefe a matsayin jingina ta farko da ake bukata domin sabuwar cinikayyar.

 Adadin ya dogara ne da muhimman jerin kudade biyu, farashinsa na yanzu, dakuma adadin rabo (ko dandazo) da akayi cinikayyar su. Girman dandazo a koda yaushe yana nufin kudade masu tushe.

 Misali, ace kabude dan karamin asusun da yake samarda 200:1 kudin aro ko 0.5% jingina. Karamin asusu yana cinikayyar karamin dandazo.

 Kamar muce dandazo daya daidai yake da $10,000.

 Idan da ace zaka bude karamin dandazo daya, maimakon ace sai ka samar da cikakkun $10,000, to abunda kawai zaka bukata shi ne $50 ($10,000 x 0.5 = $50).

 Kudin Aro

 Kudin aro shine rabon adadin jarin da akayi amfani dashi a mu’amala zuwa ga wanda ake bukatar a ajiye (“jingina”).

 Ita ce dama ta kula da adadin dala mai yawan gaske ta na’urar kudi da dan karamin adadi na jari.

 Jarin aro ya bambanta da ban mamaki da dillalai daban daban, wanda yafara daga 2:1 zuwa 500:1.

 Yanzu tunda ka burge wanda kake so da yaren kasuwancin canjin kudi, me zai hana a nuna musu iri daban daban na tsarin cinikayya?

Kara

Follow

Support this user by tipping bitcoin - How to tip bitcoin?

Send bitcoin to this address

Comment (0)

Advertisements