Hanayayin daban daban na cinikayyar kudi.


Humbleguy882022/01/13 14:31
Follow

Hanayayin daban daban na cinikayyar kudi.

WikiFX   |   2021-12-27 17:01:05

 Saboda kasuwar canji akwai kayartarwa acikinta, yan kasuwa sun samar da hanyoyi daban daban na zuba jari a kasuwar kudi.

 Acikin na’urorin kasuwar kudi, wanda sukafi suna sune retail forex, spot FX, currency futures, currency options, currency exchange-traded funds (or ETFs), forex CFDs, dakuma forex spread betting.

image_hanayayin.png

 Yanada matukar muhimmanci muyi nuni dacewa mun tattare hanyoyi daban daban wadanda dan kasuwar sodore zai iyayin kasuwancin kudi dasu.

 Kudaden Zaman Gaba

 Zaman gaba kwantiragi ne na saye da sayarda wata kadara a kayyadadden farashi alokaci maizuwa. (shiyasa ake kiransu da na zaman gaba!).

 Kudade na zaman gaba kwantiragi ne daya kunshi cikakken farshin da za’a saya da sayarda kadara a kayyadadden lokaci na canji.

 Chicago Mercentiles Exchange (CME) su suka kirkiri Kudaden zaman gaba a shekarar 1972 lokacin ana yayin wando fantalo dakuma dunduma dunduman takalma.

 Tunda kwantiragin zaman gaba an daidaita shi kuma ana kasuwancinsa a macanja ta guri daya wadda ake kula da ita, saboda haka kasuwar akwai aminci da kula acikinta.

 Hakan yana nufin farashi da hadahadar labarai a bayyane suke.

 Zaka iya kara samun ilimi akan CME’s FX na zaman gaba anan.

 Kudaden Zabi

 “Zabi” na’urar kudi ce da take bawa mi sayen kaya dama ko zabi, bawai tilastawa ba, na saye ko sayarda wata kadara a kayyadadden farashi a zabin ranar daina aiki.

 Idan dan kasuwa ya “siyarda” zabi, to zai zame masa/mata dole ya sayi ko siyar da kadara a kayyadadden farashi a adadin kwanakin daina aiki.

 Kamar dai na zaman gaba, zabi suma ana cinikayyarsu a macanja, kamar su Chicago Mercentiles Exchange (CME), the Internatonal Securities Exchange (ISE), ko kuma a Philadelphia Stock Exchange (OHLX).

 Sai dai kuma, matsalar cinikayyar zabi shi ne lokutan kasuwar yan kalilan ne na wadansu zabin, sannan yawan cinikayyar bashi da girma kamar na zaman gaba dakuma kasuwar nan da nan.

 Kudade na ETFs

 Kudade na ETF suna bada damar bude ido akan kudi ko tarin kudade.

 Kudaden ETFs suna bawa mutum dama ya bude ido a kasuwar canji ta cikin kudaden da ake sarrafawa batare da dora nauyin cinikayyar mutum daya ba.

 Kudade na ETFs za’a iya amfani dasu wajen neman Karin jari, fadada jari ko kariya daga hadarin kudade.

 Wannan shi ne jerin kudaden ETFs mafiya suna.

 ETFs an kirkiresu ne kuma ana tafiyar dasu ta hanyar cibiyoyin kudi da suke siya dakuma rike kudade acikin asusu. Sannan suna nunin nufi da hannayen jari na asusu ga jama’a a wajen canji wanda hakan yake bada dama a siya kuma ayi cinikayyar wadannan hannnayen jari kamar dai kayayyaki.

 Kamar kudaden zabi, an iyakance cewa a cinikayyar kudaden ETFs, Kasuwar ba abude take ba tsawon awa 24. Sannan kuma, kamashon cinikayya da sauran kudaden hadahada suna shafar ETFs.

 Kasuwar canji ta nan da nan. (Sport FX)

 Kasauwar canji ta nan da nan kasuwa ce ta “katse-canji” kuma ana kiranta da suna kasuwar “bisa kanta”.

 Kasuwar katse canji kasuwa ce mai girman gaske, wadda take habaka, sannan kuma mai yawan cinikayyar kudi wadda take aiki tsawon awa 24 a rana.

 Bawai kasuwa ce irinta gargajiya ba, saboda babu wani cikakken matsuguni na cinikayya ko canji.

 Ba kamar kudaden zaman gaba ba, ETFs, da kuma mafiya yawa daga cikin kudaden zabi, wadanda ake cinikayyar su ta hanyar kasuwannin da ake saka ido akansu, kasuwar canji ta nan da nan anayin kasuwancinta ne a karkashin kwantiragin bisa kanta. (yarjejeniya ce mai zaman kanta a tsakanin al’umma guda biyu).

 Da yawa daga cikin cinikayyar anayinta ne ta hanyar cibiyoyin sadarwa na na’urorin wutar lantarki (ko tangaraho)

 Kasuwar canjin kudi ta farko ita ce ake kira da “kasuwar diloli” wadda diloli suke cinikayya a tsakaninsu.

 Dila shi ne dillalin kudi wanda yakasance a shirye yake domin ya saya ko ya sayar da kudade a kowanne lokaci tare da abokanan cinikayyarsa.

 Kasuwar diloli ana kuma kiranta da sunan “kasuwar bankuna” saboda kasancewar bankuna sun mamaye kasuwar a matsayin dillalan kasuwar kudi.

 Cibiyoyin da suke cinikayya mai girman gaske kuma suke da cikakken jari mai girma sune kawai suke da ikon shiga Kasuwar diloli.

 Wannan sun hada da bankuna, masana’antun inshora, asusun fansho, manyan kungiyoyi da kuma wasu manyan cibiyoyin kudi, su suke kula da hadarurruka da suke tattare da canjin farashin kudade.

image_hanayayin1.png

 A kasuwar canji ta nan da nan, dan kasuwar cibiya yana saye da sayarwa akan yarjejeniya ko kwantiragi yana kai kudade ko ya karbesu.

 Kasuwar canji ta nan da nan yarjejeniya ce (tsakanin al’umma guda biyu) ta yadda zasuyi musayar kudade a zahiri, su canja kudi daya abisa wani kudin.

 Wannan yarjejeniya kwantiragi ce. Hakan yana nufin kasuwar canji ta nan da nan alhaki ya ratayu akanta na ta sayi kuma ta sayar da wani adadi na kudaden kasashen waje, a farashi wato “farashin canji na nan da nan” ko kuma akan farashin canji a halin yanzu.

 Saboda haka idan kasayi EUR/USD a kasuwar canji ta nan da nan, kana cinikayya ne a karkashin “kwantiragi” wanda ya kayyade cewa zaka samu wani kayyadadden adadin euro wajen musayar sa da U.S dollar akan farashin da akayi yarjejeniya akai (ko farashin canji).

 Abune mai muhimmanci kasan cewa “bazakayi” cinikayyar wadannan kudade da aka ambataba dakansu ba, saidai cewa kwantiragi ne daya kunshi wadannan kudade da aka ambata.

 Duk da cewa ana kiransa da kasuwanci na nan da nan, hadahadar bata kammaluwa a “kasuwar nan da nan”.

 A zahiri, a yayin da kasuwancin nan da nan da akeyinsa akan farashin kasuwa maici ayanzu, ainahin hadahadar bata karewa har sai bayan ranakun kasuwa biyu.

 Wannan shi ake kira da T+2 (‘’yau da kuma Karin kwanaki biyu na kasuwa’’).

 Hakan yana nufin isowar abunda ka siya ko kasiyar bazai karaso wajenka ba sai cikin kwanakin aiki biyu sannan kuma shi ake kira da muhimmin kwanan wata ko ranar karasowar sako.

 Misali, cibiya ta sayi EUR/USD a kasuwar kudi ta nan da nan.

 Kasuwancin da aka budeshi kuma aka rufeshi ranar litinin yanada ranar laraba a matsayin ranar karasowar sako. Hakan yana nufin kudaden euro zasu karaso wajensa ranar laraba.

 Ba kowanne kudade ne suke daidaituwa a T+2 ba. Misali, USD/CAD, USD/TRY, USD/RUB and USD/PHP ranar karasowar sakonsu shi ne T+1, ma’ana kwana daya na kasuwanci bayan wannan ranar ta yau (T).

 Cinikayya a ainahin kasuwar canjin kudi ta nan da nan, bashi ne wajen da yan kasuwar sodore suke cinikayya ba.

 Cinikin Sodore na Kasuwar Kudi

 Akwai kasuwar OTC ta biyu wacce take samarwa da (“talakawan”) yan kasuwa hanyar da zasuyi kasuwanci a kasuwar kudi.

 Masu samar da hanyoyin cinikayya su suke bada damar shiga.

 Masu samar da hanyoyin cinikayya sunayin cinikayya ne a kasuwar OTC ta farko amadinka. Suna samo ingantattun farashi sannan su kara “nasu Kason” kafin su sanar da farashin a manhajojinsu na cinikayya.

 Wannan yayi kama da yadda shagon dillalai suke siyo kaya daga manyan kasuwanni, su kara nasu Kason (riba) sannan su sanar da farashinsu na sari ga masu siya.

 Masu samar da hanyoyin cinikayya ana kiransu da “ Dillalan kasuwar canji”.

 A zahiri, ba dillalai bane ba, domin dillali kamata yayi ya yazama dan tsakiya tsakanin mai saye da sayarwa (tsakanin al’umma guda biyu). Amma anan ba haka abun yake ba, saboda kuwa Masu samar da hanyoyin cinikayya suna aikine a matsayin takwarorinka. Wannan yana nufin idan kaine mai siya, suna aikine a matsayin masu siyarwa. Sannan idan kaine mai siyarwa, suna aikine a matsayin masu siya. Dan a saukaka abun ake amfani da sunan “dillalan kasuwar canjin kudi”. Tunda shi ne abunda mutane da yawa sukafi sabawa dashi amma yanada kyau asan bambancin.

 Duk da cewa a kasuwar canji ta nan da nan tanada bukatar isar sako acikin kwana biyu na al’ada, babu wanda yake amsar kudi a zahiri a kasuwar cinikayyar kudi.

 Ana kuduro da matsayar ne ranar amsar kudi.

 Musamman a kasuwar sodore ta kasuwar canjin kudi.

 Ka tuna cewa, kana cinikayyar kwantiragi ne da zaka isar da muhimman kudade, amaimakon kudaden dakansu.

 Bawai kwantiragi bane kawai, a’a kwantiragi ne na rancen jari.

 Yan kasuwar kudi na sodore baza su iya “karba ko bayarwa” a karkashin rancen jari na kasuwar canji ta nan da nan ba.

 Rancen jari yana bada dama ka iya juya manyan kudade alhali kudadenka kalilan ne.

 Yan kasuwan canjin sodore suna bada dama kayi cinikayyar akarkashin rancen jari wanda shiyasa zaka iya bude matsayar darajar data ninka ainahin kudin da ake bukata sau 50.

 Saboda haka da $2,000, zaka iya bude cinikayyar EUR/USD da takai $100,000

 Ka kaddara cewa kudadenka na EUR/USD sunyi karanci kuma kana bukatar bayarda kimanin euro $100!

 Baka da damar samar da matsayar kwantiragin ta hanyar kudade, tunda abunda kawai kake dashi shi ne $2,000 a asusunka. Bakada isasshen kudin da zaka cikasa wannan hadahadar kasuwancin.

 Saboda haka sai ka rufe cinnikayyar kafin ta daidait ko kuma kasake zuba jari.

 Domin kiyaye fadawa wannan abun kunya na bayarwa ta zahiri, yankasuwar canji na sodore kai tsaye zasu juya maka.

 A yayin da kasuwancin canji ba’a bayar dashi a zahiri saidai an juyashi ne har aka rufe cinikayyar, shi ake kira da “juya cinikayyar kasuwancin canji ta nan da nan” ko kuma “juya kwantiragin kasuwar canji”

 Wannan ita ce hanyar kubuta daga tilastawa ta karbar (ko bayar da) euro 100.

 Cinikayyar kasuwancin sodore ana rufeta ne ta hanyar shiga cikin cinikayyar daidai amma kuma mai kishiya da dillalan kasuwanci canjin ka.

 Misali, idan kasiyo Fam din Birtaniya da dalar Amurca, zaka rufe cinikayyar ne ta hanyar sayar da Fam din Britaniya domin dalar Amurca.

 Wannan shi ake kira da biyan diyya ko yawaita hadahadar cinikayya.

 Idan kanada matsaya data rage a bude a lokacin rufe ranar kasuwa, kai tsaye zata cigaba da daraja ta gaba saboda kariya daga bayarda kudade.

 Yan kasuwar ka na sodore na kasuwar canji kai tsaye zasu cigaba da juya maka kwantiragin kasuwancin ka na nan da nan ba kakkautawa har zuwa sanda za’a rufeta.

 Hanyar da ake amfani da ita wajen juya kudade masu jeri biyu shi ake kira da “Gobe da jibi” (Tom-Next).

 Idan aka juya matsaya, hakan yana haifar da riba wacce ake biya ko ake samu a tareda dan kasuwa.

 Wannan farashin su ake kira da kudin canjawa ko kudin juyawa. Dillalin kasuwar canjinka zai kirga maka wannan kudaden sannan kodai a tura maka kudi ko kuma a cira daga cikin ma’aunin asusunka.

 Kasuwancin kudi na sodore ana daukar sa a matsayin hasashe ko caca. Ma’ana yan kasuwa suna kokarin suyi hasashe kuma su samu riba acikin motsawar farashin canji. Basa neman su dauki kudaden da suka siya ko bayar da wadanda suka siyar a zahiri.

 Cacar Shimfida

 Cacar shimfida abace da aka samota, wadda take nufin bazaka iya mallakar wasu kadarori ba sai dai kayi hasashen wani bigire kake tunanin farashin sa zai nufa, kodai sama ko kuma kasa.

 Cacar shimfida yana baka damar kayi hasashe akan inda farashi na jerin kudade biyu nagaba ya dosa.

 Farashin jerin kudade biyu da ake amfani dashi a…cacar shimfida an “samoshi ne” daga farashin jerin kudade biyu a kasuwar canji ta nan da nan.

 Ribarka ko faduwa yana danganta ne da yadda kasuwa take motsawa akan yadda ka so kafin ka rufe matsayarka sannan kuma da adadin kudin da ka kasaka a caca akan kowanne “ma’auni” na motsawar farashi.

 Cacar shimfida a kasuwar canjin kudi ana samar da ita ne da hanyar “masu samar da cacar shimfidar”

 Kash, idan kana rayuwa a U.S., cacar shimfida haramun ce. Duk da cewa FSA ta U.K., tana kula da ita, U.S. sun dauki cacar shimfida a matsayin cacar yanar gizo wanda kuma hakan haramun a yanzu.

 Kasuwar canji ta (“CFD”) an samota ne daga kudi. Abubuwan da aka samo suna bibiyar farashin kasuwa na muhimman kadarori ta yadda yan kasuwa zasu iyayin hasashe akan ko farashin zai tashi ko kuma ya fadi.

 Farashin CFD an samoshi ne daga farashin muhimman kadarori.

 CFD kwantiragi ne, a tsakanin mai samar da CFD da kuma dan kasuwa, ta yadda daya zai amince ya biya dayan bambancin daraja na jingina, a tsakanin budewa da kuma rufewar cinikayya.

 Awani kaulin, CFD caca ce akan wasu kadarori masu hawa ko sauka a daraja, tsakanin kai da mai samar da CFD kun amince cewa duk wanda yayi nasara a cacar zai biya dayan bambancin farashin kadarorin asanda suka shiga kasuwar da farashinta asanda suka fita.

 Kasuwancin canji na CFD yarjejeniya ce (kwantiragi) na canja bambancin farashi na jerin kudade biyu daga lokacin da ka bude matsayarka akan lokacin daka rufe ta.

 Farashin jerin kudade biyu an samoshi ne daga farashin kudade na kasuwar nan da nan.(ko a kalla ya zama haka). Idan ba haka ba, to akarkashin me masu samar da CFD suk jingina farashin su.

 Idan farashin ya motsa a bangaren da kayi hasashe, to zaka samu riba, idan kuma aka samu akasin haka to zakayi asara.

 A EU da UK, masu daidaito sun yanke shawarar cewa “ kwantiragin kasuwar canji ta nan da nan sun bambanta da kasuwar canji ta nan da nan ta gargajiya.

 Dalili shi ne kasancewar yadda ake jujjuya kwantiragin kasuwar canji, babu wani nufi na karbar sako a zahiri (ikon mallakin) kudade, manufar kawai itace yin hasashe akan motsawar farashi na muhimman kudade.

 Dalilin yin cinikayya a juyayyen kwantiragin kasuwar canji ta nan da nan shi ne samun budewar ido gameda canjin farashi wanda yake da alaka da muhimman jerin kudade biyu batare da an mallake su ba.

 Cinikayyar Kasuwar canji ta CFD tana samuwa ne ta hanyar “masu samar da CFD”

 Awajen Amurca,. Cinikayyar kasuwar kudi ta sodore ana yinta ne da CFDs ko cacar shimfida.

Kara

Follow

Support this user by tipping bitcoin - How to tip bitcoin?

Send bitcoin to this address

Comment (0)

Advertisements