Girman kasuwar duniya da Cinikayya


Humbleguy882022/01/12 16:06
Follow

Girman kasuwar duniya da Cinikayya

WikiFX   

 Mafi yawan cinikayya ta kasuwar duniya anayinta ne a abinda ake kira “kasuwar bankuna”.

 Ba kamar sauran sauran kasuwannin cinikayya ba kamar su Newyork Stock Exchange (NYSE) or London Stock Exchange (LSE), kasuwar cinikayya ta duniya bata da wani waje na muhalli na cinikayya.

 Kasuwar cinikayya ta duniya ana daukar ta kamar kasuwa mara muhalli saboda anayin cinikayya ne ta haryan anfani da na’ura a cibiyar sadarwa ta bankuna cikin awa ashirin da hudu a rana.

 Wannan yana nuna cewa kasuwar cinikayya ta duniya ta watsu ko ina cikin fadin duniya ba tare da ta kasance tana da muhalli ba. Cinikayya tana yiwuwa a ko ina matsawar kana ka damar shiga yanar gizo.

image_Kindergarten.png

 Kasuwar Cinikayya ta duniya itace tafi kowace kasuwar chinikayya girma da shahara a fadin duniya.

 Kuma dunbin mutane da kunigiyoyi na wurare daban-daban a fadin duniya suna ciniki a cikin ta.

 A kasuwar cinikayya ta duniya, yankasuwa zasu iya zaba su darje wanda zasuyi kasuwanci dashi wanda ya danganta da yanayin kasuwar, farashi me jan hankali, da kuma ingancin wanda zasuyi kasuwanci dashi.

 Taswira a kasa na nuni akan kudade guda bakwai da aka fi anfani dasu.

 Saboda kudade biyu suna cikin kowane ciniki, tarin yawan adadin kowane kudi shine 200% maimakon 100%.

 Dalar Amurka itace kudin da akafi amfani da ita wanda ya dauki kaso 84.9% na duka cinikayya.

 Kaso na Euro shine na biyu wanda ya dauki 39.1%, wanda shi kuma Yen ya zama na uku da kaso 19.0%.

 Kamar yadda kuka gani, wayannan manyan kudade suke suke sama a wannan tsarin sunaye.

 Dala itace sarauniya a kasuwar cinikayya ta duniya.

image_Kindergarten1.png

 Zaka fahimci cewa muna yawan ambaton Dalar Amurka( USD).

 Idan USD itace daya bisa biyu na kowane kudade guda biyu, kuma manya sun dauki kaso 75% na duka cinikayya, dole a maida hankali wajen dalar amurka. USD itace sarauniya!

image_Kindergarten2.png

 A zahiri ma, a fadar kungiyar bada lamuni ta duniya (IMF), dalar amurka ta dauki kimanin kaso 62% na ma’adanan kasuwar cinikayya ta duniya!

 Ma’adanan kasuwar duniya dukiya ce da ake adanata a bankin kasa a kudaden kasashen waje.

 Saboda kusan kowane me juya kudi, dan kasuwa da bankin kasa suna da ita , suna bada mahimmanci da dalar amurka.

image_Kindergarten3.png

 Akwai sauran dalilai masu karfi da suka saka Dalar amurka take taka rawar gani a kasuwar duniya, sun hada da:

 Tattalin arzikin amurka shine yafi KOWANNE a fadin duniya.

 Dalar amurka itace kudin ajiya na duniya.

 Amurka itace tafi kowacce girma da yawan cinikayya a fadin duniya.

 Amurka tana da tsayayyen tsarin siyasa.

 Amurka itace tafi kowace kasa karfin sojoji

 Dalar Amurka itace abin cinikayya tsakanin kasashe. Kamar misali man fetur ana bashi farashi a dalar amurka. Kuma ana kiran shi “petrodollars.” Idan Mexico tana san siyan man fetur daga Saudi Arabia, zata iya siya ne kawai da dalar amurka. Idan Mexico bata da dala, seta sayar da pesos ta sayi dalar amurka.

image_Kindergarten4.png

 Hasashe a kasuwar cinikayya ta duniya.

 Abu daya da za’ayi la’akari dashi a kasuwar cinikayya ta duniya a lokacin da huldar kasuwanci da cinikayyar kudade suke daga cikin girman cinikayya, yawancin cinikayyar kudade ta ta’allaka ne ga Hasashe.

 A wani fadin, yawancin gundarin cinikayya girman cinikayya yana zuwa ne daga yan kasuwa da suke saye da sayarwa a kankanin lokaci na canjin farashin kudade.

image_Kindergarten5.png

 Masu hasashe sun dauki sama da kaso 90% a abinda yake jawo girman kasuwa.

 Taswirar kasuwar cinikayya ta duniya yana nuna girman saya da sayarwa dake faruwa a lokaci yana da girma.

 Wannan yasa ya zama abu me sauki da kowa zai iya siya kuma ya sayar da kudade.

 A wajen dan kasuwa, yawan saya da sayarwa yana da amfani saboda yana nuna yadda farashi yake canzawa a cikin wani lokaci.

 Yawan saya da sayarwa a wuri kamar kasuwar cinikayya ta duniya yana kawo girman ciniki sosai a qanqanin canjin farashi.

 A sanda kasuwar cinikayya ta duniya take da yawan ciniki, zurfin kasuwa yana iya canzawa ya danganta da kudaden da ake cinikayya da kuma lokacin.

 A lokacin mu na cinikayya a kasuwar duniya na makarantar mu, zamuyi bayani akan yadda lokacin ciniki yake shafar kudaden ka kake cinikayya dasu.

 A wannan lokaci bari mu koyi yadda mutane daban daban zasu iya cinikayyar kudade.

Kara

Follow

Support this user by tipping bitcoin - How to tip bitcoin?

Send bitcoin to this address

Comment (0)

Advertisements