WikiFX: Yadda zaka samu kudi a cinikayyyar kasuwar canjin kudi


Humbleguy882021/12/30 13:36
Follow

WikiFX: Yadda zaka samu kudi a cinikayyyar kasuwar canjin kudi

Yadda zaka samu kudi a cinikayyyar kasuwar canjin kudi - WikiFX


WikiFX APP
Global Forex Broker Regulatory Inquiry APP
Download

Mene ne cinikayyar kasuwar canjin kudi?
Ta yaya cinikayyar kasuwar canjin kudi take wakana?
A kasuwar canjin kudi, ana saye da sayarda kudade daban daban.
Sanya ciniki a kasuwar canjin kudi abune mai sauki. Makanikan cinikayya sunyi kama da wanda suke acikin ragowar kasuwannin kudi (kamar kasuwar kayayyaki), sabodsa haka idan kanada ilimi ko sani a cinikayya, nan da nan zaka gane yadda abun yake.
image_stage1.0.png
Koda baka da sani ko ilimi a abun, nan da nan zaka gane harkar…. da zarar kagama makarantar Pipsology, takardar shirin koyarda cinikayyar kasuwancin kudi wadda muka samar.
Dalilin cinikayyar kasuwar canji shi ne domin yin musayar kudi daya da wani kudin alhali ana saran farashin zai canja.
Musamman ma, cewa kudin daka siya zai kara daraja akan kudin daka siyar.
Ga misali.
image_stage1.0.png
*EUR 10,000 x 1.18 = US $11,800
** EUR 10,000 x 1.25 = US $12,500
A saukake, Farashin canji shi ne kwatanta darajar kudi daya akan wani kudin.
Misali, farashin canji na USD/CHF yana nuni da yawan adadin dalolin Amurca da zasu iya siyan kudin Swiss guda daya, ko yawan adadin kudin Swiss da kake bukata kasayi Dallar Amurka daya.
Yadda ake karanta kasuwar canjin kudi
Akoda yaushe ana saka farshin kudade a jerin kudade biyu biyu, kamar GBP/USD ko USD/JPY.
Dalilin da sanya ake saka farashin su a biyu biyu shi ne, a kowacce mu'amalar canji, ana sayan kudi daya akuma sayar da wani kudin a lokaci daya.
Tayaya kake sanin kudin da zaka siya dakuma wanda zaka sayar?
Tambaya mai kyau! Anan ne inda batun kudade masu tushe da kuma kudaden da ake sakawa farashi yazo.
Kudade masu tushe da kuma wadanda ake sakawa farashi
A duk lokacin da kake da kasuwa a bude a cinikayyar kasuwar canji, to kana canja kudi daya ne domin wani kudin.
Ana sakawa kudade farashi ne a dangane da wasu kudaden.
Ga misalin farashin canjin kudin ketare na Fam din Birtaniya abisa na Dalar Amurca:
image_stage1.2.png
Kudi na farko daga bangaren dama da karan tsaye shi ake kira da kudade masu tushe (fam din Birtaniya a wannan misalin).
Kudi mai tushe shi ne muhimmiyar shaida ta farashin canji na kudade jeri biyu. Koda yaushe yanada daraja guda daya.
Lokacin siye, farashin canji yana nuni da adadin abunda zaka biya a rabo na kudade masu farashi da zaka sayi Rabo daya na kudade masu tushe.
A misalign daya gabata, farashin canji yana nuni da yawan rabo na kudade masu farashi da zaka samu idan ka siyarda Rabo daya na kudade masu tushe.
A misalign daya gabata, zaka samu dalar Amurka 1.21228 idan ka siyar da Fan din Birtaniya 1.
kudaden masu tushe suna wakiltar yawan adadin kudade masu farashi da ake bukata domin asamu rabo daya na kudade masu tushe.
Idan kasayi EUR/USD hakan yana nufin cewa kana siyan kudade masu tushe ne kuma a lokaci daya kana siyarda kudade masu farashi. A yaren mutanen farko," kasayi EUR, kasayarda USD,"
Zaka sayi jerin kudade biyu idan kayi imani cewa kudade masu tushe zasu kara daraja a dangane da kudade masu farashi.
Zaka sayar da jerin kudade biyu idan kana tunanin cewa kudade masu tushe zasu karye a dangane da kudade masu farshi.
Kasancewar da akwai jerin kudade biyu da yawa na cinikayya, ta yaya dillalan kasuwar canjin kudi suke sanin wasu kudade zasu sanya a matsayin kudade masu tushe da kuma wadanda zasu sanya a matsayin kudade masu farashi?
Anyi sa'a cewa, an daidaita yadda ake saka farashin jerin kudade a kasuwar canjin kudi.
Zaka iya kula cewa ana sanyawa kudade farashi ne a matsayin jerin kudade biyu wanda ake raba tsakanin su da alamar karan tsaye ("/").
Kasani cewa wannan al'amari ne na zabi kuma za'a iya cire karan tsayen ko a maye gurbinsa da tsawo, karan kwance ko kuma abarshi haka kawai.
Misali, wasu yan kasuwar zasu iya rubuta "EUR/USD" a matsayin "EUR-USD" ko kawai 'EURUSD". Duk gaba daya suna nufin abu dayane.
"Dogo" da Gajere"
image_stage1.3.png
Da farko, sai ka tantance cewa zaka saya ne ko kuma zaka sayar.
Idan kanaso ne ka saya (wanda yake nufin siyan kudade masu tushe dakuma sayar da kudade masu farashi), kanason kudade masu tushe suyi daraja sannan kasayar dasu a farashi mai tsada.
A yaren dan kasuwa, wannan shi ake kira "tafiya mai tsawo" ko kuma daukan "matsaya mai tsawo".
Ka tuna cewa: tsawo = saye
Idan kanaso ka sayar (wanda hakan yana nufin sayarda kudade masu tushe dakuma sayen kudade masu farashi), kanasone kudade masu tushe suyi daraja sannan ka sayar dasu a farashi mai tsada.
Wannan shi ake kirada "gajeriyar tafiya" ko kuma "gajeriyar matsaya".
Ka tuna cewa: gajere = siyarwa
image_stage1.4.png
  Ni dogo ne kuma ni gajere ne.​Shimfida ko Murabba'i
Idan bakada matsaya a bude, ana kiranka da "shimfidadde" ko kuma "murabba'I".
"Rufe matsaya" shi ake kira da "tattare murabba'i".
image_stage1.5.png
"Ni murabba'i ne."​Sa farashi, Tambaya da kuma shimfida
Gaba dayan sa farashi na kasuwar canjin kudi ana saka farashi ne guda biyu: sa farashi dakuma farashin tambaya.
A gaba daya, farashin da aka saka baya kaiwa farashin tambaya.
image_stage1.6.png
Me ake nufi da Sa farashi?
Sa farashi shi ne farashin da dillali yake da niyar sayen kudade masu tushe domin musayar kudade masu farashi.
Wannan yana nufin sa farashi shi ne farashi mafi kyawun da (kai dillali) zaka iya siyarwa a kasuwa.
Idan kanason ka siyar da wani abun, shi dillalin zai saya awajenka akan farashin da aka saka.
Mene ne "Farashin Tambaya"?
Shi Tambaya shi ne farashin da dillali zai sayar da kudade masu tushe dan yayi musayar kudade masu farashi.
Wannan yana nufin farashin tambaya shi ne farashi mafi kyawu wanda zaka iya siyayya a kasuwa.
Wata Kalmar da itama tana nufin tambaya it ace farashin nuna nufi.
Idan kanason ka sayi wani abu, dillali zai siyar da shi (ko nuna nufin) a gareka a akan farashin tambaya.
Ma ake nufi da "Shimfida"?
Bambanci tsakanin sa farashi dakuma farashin tambaya shi ake kira da suna SHIMFIDA.
A farashin da aka saka na EUR/USD a sama, farashin da aka saka shi ne 1.34568 dakuma farashin tambaya 1.34588. kayi duba da yadda wannan dillalin yasanya yadda zaka bar kudadenka cikin sauki.
Idan kanason ka sayar da EUR, sai ka danna alamar "Siyarwa" sannan ka siyar da euro dinka akan 1.34568.
Idan kanason ka sayi EUR, sai ka danna alamar "Saya" sannan ka sayi euro akan 1.34588.
Ga dan kwatance (zane) dazai tattare abubuwan da muka tattauna a wannan darasin a waje daya.
image_stage1.7.png
Yanzu bara muyi duba ga wadansu misalai.


Help

RSS

© 2020-2021 forum.forex®
The domain name forum.forex®  is a registered trade mark

Quote | 

Follow

Support this user by tipping bitcoin - How to tip bitcoin?

Send bitcoin to this address

Comment (0)

Advertisements