RAMADAN 2023


Y-IMAM2023/03/22 23:49
フォロー

MENENE AZUMI ??

RAMADAN 2023

MENE NE AZUMI...??


1. AZUMI A LUGGA

Shine kamewa


2. ASHARI'ANCE:-

Shine kamewa daga barin chi ko sha da saduwa da iyali tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.


RUKUNAN AZUMI

1. Yin niyya

2. Kamewa dagachi ko sha da saduwa da iyali

3. Zamani (lokachin yin azumi).


SUNNONIN AZUMI

1. Gaggauta buda baki

2. Jinkirta sahur

3. Addu'a yayin buda baki

4. Yin sahur da jinkirta shi.


MAKARUHAN AZUMI

1. Kaiwa matuka wajen kurkuran baki

2. Sumba

3. Dauwamar da kallo na sha' awa

4. Tunani akan al'amuran saduwa

5. Shafa ko runguma

6. Dandanan wani abu

7. Sanya tozali

8. Yin kaho.


ABUBUWAN DA SUKE BATA AZUMI

1. Saduwan wani abu zuwa makoshi (narkakke)

2. Fitarda maniyyi ko maziyyi da gangar

3. Saduwa ta hanyar tilasta

4. Chi ko sha da tunanin sauran dare

5. Chi ko sha da gangan

6. Saduwan wani abu wanda ba narkakkeba zuwa makoshi

7. Ridda.


ABUBUWAN DA SUKE HALAS

1. Yin asiwaki

2. Sanyaya jiki da ruwa

3. Tafiya ta halas

4. Sanya magani wanda ya dache

5. Tauna wani abu ga karamin yaro

6. Sanya turare.


ABUBUWAN DA AKAYI RANGWAME

1. Hadiye yawu

2. Rinjayen amai da magwas

3. Rinjayen wani kwaro zuwa ga makoshi

4. Kuran kan hanya

5. Wayan gari da janaba

6. Yin mafarki da ran.


Allah ya bamu albarkan dake cikin wannan wata na ramadan.

シェア - RAMADAN 2023

Y-IMAMさんをフォローして最新の投稿をチェックしよう!

フォロー

0 件のコメント

この投稿にコメントしよう!

この投稿にはまだコメントがありません。
ぜひあなたの声を聞かせてください。